Home Siyasa Gombe: Ka bada haƙuri ko mu dakatar da kai, APC ta faɗawa Goje

Gombe: Ka bada haƙuri ko mu dakatar da kai, APC ta faɗawa Goje

0
Gombe: Ka bada haƙuri ko mu dakatar da kai, APC ta faɗawa Goje

 

Masu ruwa da tsaki na Jam’iyar APC a Jihar Gombe sun gargaɗi tsohon gwamnan jihar, Ɗanjuma Goje a kan ya bada haƙuri ko kuma a dakatar da shi daga jam’iyar.

Jaridar Punch ta rawaito cewa jam’iyar ta baiwa Goje ƙarin wa’adin makonni biyu da ya bada haƙuri a kan rikicin da ya zama sanadiyyar rasa rayuka da asarar dukiyoyi a kwanakin baya a jihar.

Punch ta ƙara da cewa dama can jam’iyar ta baiwa Goje, wanda shine Sanata mai wakiltar mazaɓar Gombe ta tsakiya, wa’adin wata daya da ya bada haƙuri a kan rikicin da ya faru amma bai bayar ba, shine a ka ƙara masa makonni biyu inda daga nan idan ya ƙi ya bada hakurin, to zai fuskanci dakatarwa.

Da ya ke jawabi a makarantar sakandare ta Pindiga, Mohammed Kashere, shugaban APC na mazaɓar Kashere, inda nan ce mazaɓar Goje, ya ce masu ruwa da tsaki a jam’iyar ne su ka amince da a karawa Gojen wa’adin makonni biyu, in ya ki bada haƙuri, to sai a dakatar da shi a jam’iyance.