
Matashin da ya banka wa masallaci wuta a jihar Kano, Shafi’u Abubakar ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa a gaban kotu.
Abubakar, mai shekara 39, wanda ya gurfana a gaban wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke unguwar Rijiyar Zaki a birnin Kano, an tuhume shi da laifuka uku, inds ya ce ya amince da tuhume-tuhumen da aka karanta masa.
A ranar Laraba, 15 ga watan Mayu ne dai matashin ya cinna wuta a wani masallaci da ke ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar Kano, daidai lokacin da ake tsaka da sallar asuba, inda kusan mutane 30 suka kone.
Yanzu haka mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar wutar sun kai 17, yayin da wasu mutum 12 ke kwance a asibiti.
Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa 31 ga wannan Mayun da mu ke ciki domin bai wa wanda ake zargi damar samun lauya, sannan masu gabatar da kara su samu damar tattara shaidu.
BBC Hausa