Daga Mahmud Isa Yola

Shiga Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama Na Hilf al-fudul Da Manzon Allah SAW Yayi

A lokacin jahiliyya, a cikin garin Makka kuma a karkashin mulkin jahiliyya, Manzon Allah SAW ya shiga wata kungiya da ake kira da Hilf al-fudul. Kungiyar tana fafutukar kawo zaman lafiya da kuma bi wa duk wanda aka tauye wa hakki hakkin sa a cikin garin Makka.

Har lokacin da musulunci ya kafu a garin Madina da Makka, Manzon Allah SAW bai bar kungiyar ba. Talha dan Abdallah yake cewa “idan da an sake gayyatan Manzon Allah zuwa makamancin kungiyar a lokacin da Musulunci ya mamaye garuruwan Makka da Madina da zai amsa gayyata kuma ya shiga kungiyar.” (Sunanul Kubura 12114, Aldala’il Gharib 243).

Ibn Hashim yace su ‘yan kungiyar na Hilf al-fudul sun yaddan wa kansu cewa babu wani wanda za’a tauye wa hakki cikin mutanen su ko kuma duk wanda ya shiga garin Makka ba tare da sun bi masa hakkin shi ba.(Musnad Ahmad 2904).

Saboda haka ne malamai suka cewa musulmai, ko da a wuraren da basu ne ke rike da gwamnati ba, yakamata su kasance suna kwatanta gaskiya kuma suna kin duk wani abu da bai dace ba a gwamnatance iya gwargwado. Wannan yana nuna mana yin amfani da addini wajen tozarta wasu ko da ba musulmai bane babban kuskure ne kuma sabawa Allah ne da Manzon Sa.

Mu hadu a fitowa na gaba.

(ABUN LURA: wannan rubutu na guzurin Ramadan zai rika zuwa muku a shafukan jaridun Hausa tareda marubuci Mahmud Isa Yola)