Home Labarai Gwamna Fubara na jihar Rivers, yaron Wike, ya samu nasara a Kotun Ƙoli

Gwamna Fubara na jihar Rivers, yaron Wike, ya samu nasara a Kotun Ƙoli

0
Gwamna Fubara na jihar Rivers, yaron Wike, ya samu nasara a Kotun Ƙoli

Kotun Daukaka kara da ke zamanta a jihar Legas ta tabbatar da zaben Siminalayi Fubara a matsayin gwamnan jihar Rivers.

Kotun ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar, Patrick Tonye-Cole, ya shigar da Fubara na jam’iyyar PDP da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

A zaman kotun na yau Talata, dan takarar jam’iyyar APC ya bukaci kotu da ta umarci INEC da ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Rivers da aka gudanar a watan Maris.

Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Rivers ce ta kori karar Cole da ke neman a ta kori Fubara a matsayin gwamna a farkon watan Oktoba.

Rashin gamsuwa da hukuncin kotun, dan takarar APC ya garzaya kotun daukaka kara.

Sai dai kotun a yau Talata ta amince da hukuncin tirabunal din, wanda ya tabbatar da nasarar Fubara a watan Oktoba.