Wakilin gidan radiyo freedomAbbas Yushau

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umarnin a sallami wakilin gidan rediyo freedom daga aiki a fadar gwamnati.

Wakilin gidan rediyo freedom dake fadar gwamnatin Kano Abbas Yusha’u Yusuf ya gamu da fushin gwamnan ne sakamakon wani labari da ya bayar da bai yi wa gwamnan dadi ba, dan haka ba tare da bata lokaci ba, gwamnan yasa aka kore shi daga gidan gwamnati.

Abbas Yushau dai na cikin tawagar Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje a lokacin da tawagar tayi arba da ‘yan fashi akan hanyar zuwa Jos.

A don haka ne, Abbas dake zaman daya daga cikin ‘yan jarida da suke bin tawagar gwamna, ya shirya rahoton abinda ya faru a artabun da tawagar gwamnan tayi da ‘yan fashin.

Ya bayar da labarin yadda Gwamnan da mai dakinsa ssuka hau jirgi mai saukar ungulu suka tsre zuwa Abuja, yayin da Gwamnan ya kyale dukkan ‘yan tawagarsa da suke masa rakiya suka bi hanya domin komawa Abuja.

Ance wannan labari da dan jaridar gidan Rediyo Freedom ya bayar bai yiwa Gwamna dadi ba.

A saboda haka ne, Gwamnan yana komawa Abuja, ya sanar da daraktan yada labaransa, Salihu Tanko Yakasai da cewar a sallami wakilin Rediyo Freedom daga gidan gwamnati, a cewar gwamnan, wannan labarin ya zubar masa da kima, musamman irin yadda takwarorinsa gwamnoni ke masa magana kan batun.

A nasu bangaren, gidan Rediyo Freedom sun ki yadda da bukatar gwamnatin Kanon na janye wakilinsu daga fadar gwamnati. Suna masu tabbatar da cewar, babu wani laifi da waiklin nasu yayi don ya bayar da labarin abin day a faru da tawagar gwamnan ba tare da yayi Karin gishiri ba.

Tun da abin ya faru har ya zuwa yanzu dai, Rediyo Freedom basu amsa bukatar gwamnan ba, kuma dai basu tura wani sabon wakili zuwa gidan gwamnatin ba.

A wani kaulin kuma, ance Gwamna Ganduje da kansa ya kira gidan rediyon yake umartarsu da su janye wakilin daga fadar gwamnati su kawo wani wanda ba Abbas Yushau ba.

Ko ya kuke ganin zata kaya tsakanin gidan rediyo freedom da Gwamna Abdullahi Umar Gwanduje?