
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya amince da sayan taki na kimanin Naira biliyan 5.07 domin tallafawa kananan manoma a jihar.
Wannan yunkuri na da nufin saukaka wadatar abinci a matsayin sabon tsarin ci gaban noma a jihar.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar a Kano a yau Talata, an ba da amincewar ne yayin taron majalisar zartarwa ta jiha karo na 15, SEC.
“Za a raba takin ne a fadin kananan hukumomi 44 domin tallafa wa manoma musamman na karkara domin kara yawan amfanin gona a kakar damina ta 2024,” inji shi.
Ya bayyana cewa za a sayar wa manoman takin ne a kan farashi mai rahusa, wanda hakan ke nuna aniyar gwamnan na samar da kayan amfanin gona masu inganci da araha.
Wannan matakin ya biyo bayan siyan hatsi na biliyoyin naira a baya da gwamnan ya yi, inda aka raba wa marasa galihu a jihar domin rage raɗaɗi.