
Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya raba dabbobi dubu biyar ga ƴan gudun hijira 2,500 a Pulka da ke karamar hukumar Gwoza ta jihar.
Zulum ya bayyana haka ne a wajen bikin kaddamar da rabon dabbobin a jiya Alhamis a Pulka.
Gwamnan, wanda mataimakinsa Usman Kadafur ya wakilta, ya ce an raba dabbobin ne ga manoman da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, domin su samu damar mayar da dabbobinsu da kuma inganta rayuwarsu.
Ya ce hakan na daga cikin kokarin gwamnati na maido da ababen more rayuwa da ‘yan gudun hijirar suka rasa.
A cewarsa, gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar abokan hulda na aiwatar da tsare-tsare masu inganci don dawo da rayuwa da inganta rayuwar al’umma bisa tsarinta na raya kasa da kuma ajandar kawo sauyi na shekaru 10.
Zulum ya yabawa hukumar tabbatar da zaman lafiya ta yankin da kuma shirin raya ci gaba na Majalisar Dinkin Duniya, UNDP, saboda goyon bayan da suka bayar wajen samun nasarar aiwatar da shirin.
Ya kuma umarci wadanda suka amfana da su kula da dabbobin domin inganta zamantakewa da tattalin arziki.