Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru el-Rufai yayin da yake sanya hannu a takardun shigar da Sanata Datti Baba-Ahmed kara a babbar kotun jihar Kaduna

A ranar talata Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru el-Rufaia ya shigar da kara babbar kotun jihar Kaduna, yana mai karar tsohon Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed a kotu bisa abinda Gwamnan ya kira da bata suna da tsohon Sanatan yayi masa.

Gwamnan ya shigar da karar, yana mai rokon kotun da ta sanya tsohon Sanatan ya biyashi diyyar Naira Biliyan daya akan bata masa suna da Sanatan yayi a cewar Gwamnan jihar Kadunan Malam Nasiru el-Rufai.

Idan ba’a manta ba, a ‘yan kwanakin da suka gabata ne tsohon Sanatan ya sallamar jam’iyyarsa ta APC zuwa jam’iyyar PDP a jihar Kaduna. Shi dai Sanata Datti Baba-Ahmed ana yi masa kallon daya daga cikin jigon jam’iyyar APC a  jihar ta Kaduna.

Shi dai Sanata Datti Baba-Ahmed ya zama Sanata bayan da ya kayar da tsohon Gwamnan jihar Kaduna karo biyu, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi.