Gwamna Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganudje ya nuna damuwa kan matakin da mataimakinsa Farfesa Hafizu Abubakar ya dauka, dangane da wasu abubuwa da yace anyi masa a jam’iyyarsu ta APC.

Gwamnan ya kuma bukaci a mayar da duk wanda aka cire kan mukaminsa a cikin jam’iyyar, kamar yadda mataimakin Gwamnan yayi korafin an cire kaninsa daga shugabancin mazabarsu ta Mandawari a yankin karamar hukumar Gwale.

Masu fashin bakin siyasa dai na cewar tuni aka samu baraka a jam’iyyar APC reshen jihar Kano, yayin da a gefe guda mutanan tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso suke yabawa matakin da mataimakin Gwamnan ya dauka.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yace ayi duk abinda ya kamata domin kaucewa faruwar baraa domin kuwa zabe na kara karatowa a cewar Gwamnan.