Home Labarai Gwamnan Kano ya rantsar da sabon kwamishina a sabuwar ma’aikatar tsaro ta jiha

Gwamnan Kano ya rantsar da sabon kwamishina a sabuwar ma’aikatar tsaro ta jiha

0
Gwamnan Kano ya rantsar da sabon kwamishina a sabuwar ma’aikatar tsaro ta jiha

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya rantsar Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris Mai Ritaya a matsayin kwamishinan tsaro na cikin gida.

Gwamnan ya rantsar da tsohon Janar na sojan ne a yau Juma’a a fadar Gwamnatin Kano.

Janar Muhammad, zai jagoranci sabuwar ma’aikatar tsaro da gwamnatin ta samar.

Hakan dai na zuwa ne bayan majalisar dokoki ta amince da nadin nasa.