23.1 C
Abuja
Tuesday, February 7, 2023

Gwamnan Osun mai barin-gado ya naɗa manyan sakatarori 30 saura kwanaki 3 ya bar mulki

Must read

A jiya Alhamis ne gwamnan jihar Osun mai barin-gado, Adegboyega Oyetola, ya nada ma’aikatan gwamnati 30 a matsayin Sakatarorin Dindindin, wanda a ka fi sani da ‘Parmanent Secretary’.

Sunayen wadanda aka nada na kunshe ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan, Dr Festus Oyebade.

Sanarwar ta ce wadanda aka nada za su cike guraben da ake da su a ma’aikatan gwamnatin jihar.

Sai dai zababben gwamnan jihar Osun mai-jiran-gado, Ademola Adeleke, a wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, ya gargadi wadanda aka nada mukamin.

Sanarwar ta kara da cewa, “Muna so mu sanar da cewa wadanda su ka amince da nadin su kasance a shirye cewa za su bar aikin ko wa’adin aikinsu ya kai shekarun da su ka gabata ko a’a.

“Za a dauka cewa wannan muƙamin kawai na siyasa ne wadanda za su bi gwamna mai barin-gado kai tsaye daga aikin gwamnati daga ranar 28 ga Nuwamba.

“Haka kuma, wadanda har yanzu suke son ci gaba da yi wa Gwamnatin Jihar Osun hidima su yi watsi da wannan naɗin muƙamin na jeka-na-yi-ka da Gwamna mai barin-gado ya ba su. Mun tabbatar da cewa ba za mu ji wani ɗar wajen korar duk wani sakatare na dindindin na bogi ba,” in ji shi.

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article

- Website Designed By DEBORIAN.COM, a Nigerian Web Designer and Web Developer -