
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya ce gwamnatinsa ta dukufa wajen ganin an samar da sulhu mai ɗorewa da al’ummar kudancin jihar.
Sani ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya aikewa kungiyar shugabannin Kiristocin Kudancin Kaduna na Majalisar Fastoci a Cocin Throneroom Trust da ke Kafanchan.
Gwamnan, wanda ya samu wakilcin babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin addinin Kirista, Rabaran Ishaya Jangado, ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take ta gyara kura-kuran da gwamnatocin baya suka yi domin ci gaban jihar.
Ya kuma yi kira ga al’ummar kiristoci na shiyyar da su hada kai da gwamnati mai ci a yunkurinta na tafiyar da gwamnati mai tafiya da kowa.
Tun da fari, Apostle Emmanuel Kure, shugaban kungiyar shugabannin addinin Kirista ta Kudancin Kaduna, ya ce an kira taron karshen shekara ne domin yi wa kasar nan addu’a a gaba da dai sauransu.
Kure ya yabawa gwamnan bisa kokarinsa na hada kan jihar tare da yin alkawarin goyon bayan kungiyar kan shirye-shiryen da suke da shi na inganta zaman lafiya a addini a jihar.