Home Labarai Gwamnatin Cross River za ta yi wa jiragen ruwa rijista domin daƙile garkuwa da mutane a ruwa

Gwamnatin Cross River za ta yi wa jiragen ruwa rijista domin daƙile garkuwa da mutane a ruwa

0
Gwamnatin Cross River za ta yi wa jiragen ruwa rijista domin daƙile garkuwa da mutane a ruwa

 

Gwamnatin Cross River ta ce tana nan tana shirye-shiryen fara yi wa kwale-kwale da sauran jiragen ruwa rijista domin magance garkuwa da mutane a ruwa.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Bobby Ekpenyong, Darakta-Janar na hukumar kula da ruwa ne ya baiyana haka a ranar Laraba.

Ekpenyong ya baiyana cewa masu harkar jiragen ruwan za a basu lasisi a karshen aikin yin rijistar da za a fara a ranar 1 ga watan Disamba.

Ya ce yin rijistar na da matuƙar amfani duba da yawan matsalolin garkuwa da mutane da sauran aiyukan ɓata-gari a kan ruwa.

“Gwamna Ben Ayade ya damu da yawan garkuwa da mutane da kuma aikata sauran laifuka a kan ruwa.

“Ya bada umarnin a ɗauki matakan da su ka dace.

“Zan yi amfani da wannan dama na gargaɗi duk masu harkar kwale-kwale, jiragen ruwa masu na’urar lantarki da sauransu cewa za mu kwace duk wani jirgi da ba a yi masa rijista ba daga nan zuwa 1 ga watan Janairu,”