Gwamnan jihar Bunuwai, Samuel Ortom

Gwamnatin jihar Bunuwai ta musanta daukar nauyin wasu ‘yan sintiri da suka ce ita ce ta basu makamai domin aikin tsaro a jihar, bayan kama su da rundunar soja suka yi.

Daraktan yada labarai na Gwamnan jihar, Mista Terver Akase, ya fitar da wata sanarwa da take cewar “Muna fada da kakkarfar murya, Gwamnatin jihar Bunuwai karkashin jagorancin Gwamna Samuel Ortom bata dauki wani dan sintiri yayi aiki da sunanta ba tunda Gwamna ya kama aiki”

Mista Akase yace, An shaidi Gwamnan Ortom da kasancewarsa mai son zaman lafiya, kuma tun farkon zuwansa Gwamnati ya bayyana yin afuwa ga masu dauke da makamai domin samar da zaman lafiya a jihar.

Yace, hakan ta sanya sama da matasa 800 da suke kungiyoyin ‘yan ta’adda daban daban suka ajiye makamansu domin karbar tayin zaman lafiyar da gwamnan yayi musu, hakan ta sanya aka ajiye sama da makamai 700.

“Gwamnatin jihar Bunuwai bata taba yin amfani da jami’an tsaron da ba na Gwamnatin tarayya ba wajen baiwa rayuwar al’umma da dukiyoyinsu kariya ba. Ko a wannan harin baya bayan nan da Makiyaya suka kaiwa jama’a a gonakinsu a karamar hukumar Logo da Guma, Gwamna bai yadda jama’a su dauki doka a hannunsu ba”

“Gwamnan Bunuwai mai son zaman lafiya ne, kuma yana aiki da dukkan hukumomin tsaro domin samar da tsaro a dukkan fadin jihar”

“Haka kuma, Gwamna bai yi komai ba sai da sahalewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen kara masa yawan jami’an tsaro a jiharsa”

NAN