Gwamnan jihar Kaduna Mallam nasiru el-Rufai

Gwamnatin Jihar Kaduna tana jiran amincewar Majalisar Dattijai don samun bashin dala miliyan 350 daga bankin duniya.

Tuni daiBankin Duniya ya amince da ba Gwamnatin Jihar Kaduna bashin Dala miliyan 350 don inganta fannin kiwon lafiya da fannin ilimi da yin ayyuka na raya kasa. Gwamnatin Jihar Kaduna yanzu dai na jiran amincewar Majalisar Dattijai ne don samun wannan bashin.

Wannan dai bashin za a biya shi ne a cikin shekara 50 kuma ba za a fara biya ba sai nan da shekara 10 kuma bashin ba ruwa don kashi 0.5% ne kawai za a biya.

Gwamnatin Tarayya ta yaba da yadda Gwamnatin Jihar Kaduna ta gabatar da takardanta na neman wannan bashin saboda irin yadda ta cika duk ka’idojin da ake bukata.

Meye ra’ayinku kan wannan bashi da GwamnatinKaduna zata ciwo?