Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello

A ranar Larabar nan, Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya bayyana cewar, Gwamnatinsa ta kashe zunzurutun kudi Naira biliyan 4.3 domin yiwa makarantu guda 9 kwaskwarima a fadin jhar a wani shiri na inganta makarantun Gwamnati da gwamnatinsa ta bullo da shi.

Gwamnan ya shaidawa manema labarai cewar an kashe kudaden ne wajen gyara ajuzuwan da suka lalace da gyaran bandakuna da sanya kujeru a makarantun da kuma yi musu fenti.

Yakara da cewar Gwamnatin kuma ta samar da wasu kayayyakin aikin domin amfanin malaman makarantu da suka hadar da kayan lantarki da dangoginsu da kuma kujeru da tebura.

“Alokacin da muka shigo Gwamnati a 2015 mun tarar da komai kusan ya lalace,ko yana gab da durkushewa, muna da makarantun da kusan shekaru 40 basu taba ganin fenti ba, dan haka muka gyara irinsu”

“Mun tarar da wasumakarantun babu bandakuna, wasu ajujuwan sun rushe, awasu makarantun kwana kuwa, wasu babu dakunan dafa abinci da kuma inda yara zasu ci abinci, sannan dakunan kwanan duk sun lalace”

“Taya kuke zaton zamu iya samar da jagorori na gari a irin wadannan lalatattun makarantun da yara basa samun yanayin koyo mai kyau?”