24 C
Abuja
Friday, May 20, 2022

Gwamnatin Kano ta karɓe lasisin duk makarantu masu zaman kansu kan kisan Hanifa

Must read

 

Biyo bayan kisan gillar da aka yi wa wata daliba Hainfa Abubakar mai shekaru biyar, gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin karɓe lasisin gudanar da duk wasu makarantu masu zaman kansu a jihar.

Kwamishinan Ilimi na jihar, Muhammad Sanusi Ƙiru ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a ma’aikatarsa ​​a yau Litinin.

Ya ce matakin ya zama dole domin tsaftace ayyukan makarantu masu zaman kansu da kuma kare su daga duk wani abu da ya shafi muggan laifuka domin gujewa maimaicin irin wannan lamari na Hanifa.

Ƙiru ya sanar da cewa nan ba da dadewa ba za a kafa wani kwamiti mai karfi da zai sabunta lasisin, inda ya kara da cewa gwamnati za ta gindaya sharuddan aikin.

A cewarsa, duk makarantar da ta gaza cika wadannan sharudda za a rufe ta har abada.

Don haka kwamishinan ya yi kira ga mamallaka makarantu masu zaman kansu da su mika lasisin su sannan su jira sanarwa ta gaba da ga gwamnati.

Ya ce, “dukkan mu muna sane da lamarin da ke faruwa game da mutuwar Hanifa, saboda wani mutum da ake zargi mai suna Abdulmalik Tanko wanda shi ne shugaban makarantar Noble Kids Academy ya yi mata kisan gilla, kuma bisa la’akari da abin bakin ciki da ya faru, musamman dangane da yadda aka kashe ta. makarantar masu zaman kansu, gwamnatin jihar ta yanke shawarar janye satifiket na duk wasu makarantu masu zaman kansu don sake tantancewa.

A cewarsa, kwamitin zai kunshi jami’an tsaro irin su ma’aikatar tsaro ta farin kaya, DSS, NSCDC, hukumar kashe gobara da sauran hukumomin domin samun nasarar aikin.

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article