
Gwamnatin jihar Kano ta maka tsohon kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sule-Garo da ƙannensa guda biyu, Mustapha Sule-Garo da Mohammed Sule-Garo a gaban kotu, bisa tuhume-tuhume har guda bakwai kan zargin karkatar da kudaden kananan hukumomi har Naira biliyan 2.8.
A karar da babban lauyan gwamnatin jihar kuma kwamishinan shari’a ya shigar, ta hannun lauyansa, Auwal AbdulQadir-Sani, gwamnatin ta zargi wanda ake tuhuma da amfani da kudaden wajen siyan kadarori a kasar Saudiyya.
A bisa tuhume-tuhume da aka shigar a babbar kotun jihar Kano, gwamnatin jihar ta yi zargin cewa an karkatar da kudaden ne daga asusun ayyukan kananan hukumomi da kuma kashi daya bisa dari na bayar da horo.
Auwal ya ce an shigar da karar ne a karkashin sashe na 211 na kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima da kuma sashe na 121 [1], 123 [1] [a], 126 [b], da 377 na dokar shari’a ta jihar Kano [2019]. .
Mutane bakwai ake tuhuma da suka hada da tsohon kwamishinan da ‘yan uwansa da ma’aikatan ma’aikatar da kamfanoni biyu.