Gwamnan jihar Katsina Alhaji AMinu Bello Masari

Jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina, ta zargi Gwamnatin jihar karkashin Aminnu Bello Masari da barnatar da dukiyar jama’a da ta kai Naira biliyan 400 a banza cikin watanni 31 ba tare da nuna wani abun ku zo mu gani ba.

Alhaji Salisu Majigiri,Shi ne Shugaban jam’iyyar PDP a jihar Katsina, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya kira a ranar Talata a jihar Katsina. Majigiri yace, an barnatar da bibiyan 400 karkashin Gwamnatin Aminu Bello Masari.

Ya ce, duk irin makudan kudaden da Gwamnatin tarayya ta dinga antayowa jihar, amma har yanzu jama’ar jihar na fama da halin matsin rayuwa, a cewarsa, manyan jami’an Gwamnatin jihar na yin wadaka da dukiyar jama’a yadda suka ga dama.

Kamar yadda ya fada, Gwamnatin jihar ta karbi tsabar kudi sama da Naira biliyan 243 daga asusun Gwamnatin tarayya, sannan kuma ta sake karbar biliyan 30 daga asusun nan na ‘Paris club’ wanda Gwamnatin tarayya ta rabawa jihohi.

“A madadin al’umma su gani a kasa na irin wadannan zunzurutun kudin da Gwamnati ta karba, amma har yanzu mutane na kukan halin matsin rayuwa, da wadannan makudan kudade maimakon Gwamnati ta mayar da hankali wajen inganta jihar, sai ta bige da sake ciwo bashin naira biliyan 70 domin jefa al’ummar Katsina cikin mawuyacin hali”

“Muna kuma sane da cewar, gwamnati ta samu biliyoyin Nairori a harajin da take karba a cikin gida, duk da cewar Gwamnatinmu ta PDP ta tafi ta barwa wannan Gwamnati zunzurutun kudi har Naira biliyan 14.5 a cikin asusun Gwamnati” A cewarsa.

Shugaban jam’iyyar, ya cigaba da bayanin cewar, a zahirin gaskiya kudaden da Gwamnatin Katsina ta yanzu ta karba karkashin jagorancin AMinu Bello Masari, sun kai kimanin Naira biliyan 464, domin a duk wata tana samun Naira biliyan 13 daga kason gwamnatin tarayya.

“A sabida irin almundahana da wadaka da jami’an Gwamnati suke yi a Katsina, al’umma suna shiga cikin mawuyacin hali, ta yadda da yawa suka zama mabarata da ‘yan maula domin neman abinda zasu ci”

“Dukkan wani sashi na tattalin arzikin jihar Katsina tamkar anyi masa yasa, mutane basa samun takin zamanicikin sauki wanda shi ne zai taimakawa manoma da abinda zasu ci, sannan kuma hakan shi zai kara bunkasa harkar noma”

“Yanzu a halin da ake ciki, takin zamani ya zama tamkar zinare a jihar Katsina, babu wani tallafi da Gwamnati take baiwa manoma, irin alherin da Gwamnatin da ta gabata take yiwa manoma yanzu duk an dena sabida bambancin siyasa”

“Makarantun Gwamnati a jihar Katsina sun koma tamkar kufai, babu kayan aiki, babu wani hobbasa domin ciyar da ilimi gaba, babu kula da yanayin malamai, sabida kowa na tsoron za’a iya korarsa”

“Asibitocinmu sun koma matattarar tsaffin gadaje da karafa, kudaden da ake bayarwa domin inganta asibitocin duk an sace su da sunan samar da yanayi mai kyau a asibiti”

Haka kuma, a lokacin da yake mayar da martani kan zargin da PDP ta yi,mai taimakawa Gwamnan Katsina na musamman kan kafafen yada labarai Abdu Labaran, yace dukkan wadannan zarge zarge ba su da tushe balle maka.

Labaran ya cigaba da cewar, Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Aminu Bello Masari tana yin iyakar kokarinta wajen alkinta dukiyar jihar domin taimakon al’umma.

Haka kuma, ya lissafo wasu daga cikin ayyukan da yace gwamnatin tayi domin inganta rayuwar al’umma kamar, inganta manyan asibitocin Katsina da Daura da Funtuwa da Kankia.

“Wannan Gwamnati ta masari ta gyara makarantu kimanin gida 100 tsakanin karamar Sakandire da babbar Sakandire a dukkan fadin jihar”

Mista Labaran ya cigaba da cewar, Jam’iyyar PDP ta gama zangwanyewa a jihar Katsina, dukkan jiga jiganta sun tarwatse kamar tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Yau Gwajogwaji da Sanata Ibrahim Ida dukkansu sun san inda dare yayi musu, sun dawojam’iyyar APC.

Ya kara da cewar “Majigiri da ‘yan amshin shatansa, sun dimauce ne kawai sakamakon wawar asarar da PDP take fuskanta a jihar Katsina, jam’iyyar da yanzu ta zama kango babu kowa, mutanan Katsina sun ma fara mantawa da ita”

NAN