
Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da haramta sayar wa da shan Shisha da sauran abubuwan da ba na magani ba a fadin jihar.
Sanarwar dakatarwar ta fito ne a wata sanarwa da daraktan yada labaran jihar, Buhari Mamman-Daura, ya fitar ranar Juma’a a Katsina, inda ya ce hanawar ta gaggawa ce.
Ya ce dokar hana Shisha da sauran abubuwan maye, na daga cikin Dokar 2022 da Gwamna Aminu Masari ya sanya wa hannu a ranar 5 ga Satumba.
“Wannan ya yi daidai da ikon da aka ba shi a tanadin sashe na 5, karamin sashe na 2 na kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya na 1999, kamar yadda aka yi kwaskwarima.
“Da wannan ci gaban, an hana sayar da, kuma shan shisha ko mu’amala da duk wani abu da ba na magani ba musamman shisha a duk fadin jihar,” in ji daraktan.
A cewarsa, gwamnati ta dauki matakin ne duba da yadda ake samun karuwar matasa masu sha’awar shan shisha a jihar.
Ya ci gaba da cewa duk wanda ya karya wannan umarni zai fuskanci laifin da za a hukunta shi a karkashin sashe na 114 na dokar Penal Code na jihar Katsina 2021.
Kwararrun likitocin sun bayyana cewa Shisha na da irin wannan illa ga lafiya kamar yadda taba sigari ta ke kuma ta na iya haifar da matsalolin zuciya da jijiyoyin jini kamar bugun zuciya da sauran su.
Shisha kuma na da kusan adadin nicotine da sigari.