Home Labarai Gwamnatin Nijar ta janye dakatar da ayyukan hakar ma’adinai

Gwamnatin Nijar ta janye dakatar da ayyukan hakar ma’adinai

0
Gwamnatin Nijar ta janye dakatar da ayyukan hakar ma’adinai

Gwamnatin jihar Neja ta dage dakatarwar da ta yi wa duk wasu masu ayyukan hakar ma’adinai a jihar.

Mukaddashin gwamnan jihar, Yakubu Garba ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke kaddamar da kwamitin yaki da hako ma’adinai da lalata muhalli ba bisa ka’ida ba a jihar.

A cewar wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Bologi Ibrahim ya fitar, mukaddashin gwamnan ya lura cewa harkar ma’adanai na da matukar muhimmanci wajen bunkasar tattalin arziki, inda ya nuna takaicin yadda ayyukan hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ke yin illa ga muhalli a jihar.

Ya bayyana cewa daga cikin bayanan da ake da su, akwai kamfanonin hakar ma’adinai 880 da suka yi rajista wadanda suka hada da kamfanoni 578 da kuma kungiyoyin hadin gwiwa 302 a jihar.

Ya ce, duk da haka, kusan kamfanoni 261 ne kawai su ka zo dan tantancewa.

Yakubu ya bayyana kwarin gwiwar cewa rundunar musamman da aka kafa za ta aiwatar da ka’idoji tare da tabbatar da ayyukan hakar ma’adinai akan doron doka da tsare-tsaren gwamnati.