
Gwamnatin jihar Sokoto ta bukaci mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da ya rika bin diddigin gaskiyar lamari kafin ya yi tsokaci kan al’amuran da suka shafi ƙasa baki daya.
Da ta ke mayar da martani ga gargadin da Shettima ya yi a bainar jama’a a taron tsaro na yankin arewa maso yamma da aka ƙaddamar a Katsina a jiya Litinin, gwamnatin jihar ta ce kamata ya yi mataimakin shugaban kasar ya tuntubi gwamna Ahmed Aliyu domin tabbatar da labarin kan shirin tsige Sultan Muhammadu Sa’ad Abubakar kafin ya yi magana akai.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Abubakar Bawa ya sanyawa hannu, gwamnatin ta bukaci Shettima da ya kasance ya na da cikakken sanin al’amuran da suka shafi kasa baki daya kafin yin tsokaci a kansu.
“Gaskiya mun yi tsammanin Mataimakin Shugaban kasa zai tuntubi Gwamna kafin ya fito fili ya yi magana da kan batun.
“A matsayinsa na dattijon ƙasa kuma uba ga kowa da kowa, ya kamata ya kasance yana da cikakken bayani kafin yanke hukunci a kan batutuwan da ƴan adawa ke yaɗa wa ta tarkacen kafofin sadarwa da suka shahara wajen yaɗa farfaganda marasa kyau.
“Gaskiyar magana ita ce ba a taba yunkurin tsige Sarkin Musulmi ba, haka kuma ba mu aika masa da wata barazana dangane da hakan ba.
“Sultan yana jin daɗin duk wani ikon da ya cancanta. Ba mu taba hana shi wani ’yancinsa ko hakkinsa ba .
“Don haka ba ma bukatar a ce mu kare martaba da mutuncin Sarkin Musulmi. Dama can alhakin mu ne wannan,” in ji sanarwar.