
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Mohammed Idris, ya bukaci kafafen yada labarai da su rage yaɗa labaran aiyukan ta’addanci, inda ya ce hakan na karawa ‘yan ta’adda kwarin guiwa da kuma dakushe kwarin gwiwar jami’an tsaro.
Idris ya bayyana hakan ne a Abuja a jiya Talata a yayin bude taron horas da ƴan jarida na kwanaki biyu mai taken “Ingantacce Rahoto don Karfafa Akidun Ta’addanci”, wanda Cibiyar Yaki da Ta’addanci ta Kasa, NCTC, tare da hadin gwiwar Hukumar Yaki da Ta’addanci ta kasa suka shirya. Cibiyar Aminci da warware rikice-rikice.
“Yawanci, ba a ganin aikin wadanda su ke yaki da ta’addanci. Yana da mahimmanci ga dukanmu mu san cewa ’yan ta’adda ba wai yaƙin zahiri kawai suke yi ba, suna kuma faɗa na tunanin al’umma.
“Saboda haka, abin ya ba ni mamaki idan shugabannin kafafen yada labarai a wasu lokuta suna tallata ayyukan wadannan ‘yan ta’adda duk da cewa ba da angan ba. Idan babu farfaganda, ta’addanci ba zai bunkasa ba,” in ji shi.