
Gwamnatin Najeriya ta amince a rinƙa bayar da hutun haihuwa na kwana 14 ga maza masu aikin gwamnati.
BBC ta rawaito cewa Shugabar ma’aikata ta gwamnatin tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan ce ta sanar da hakan a wata takardar sanarwa da ta fitar a jiya Litinin.
Sanarwar ta ce “gwamnati ta amince da hutun haihuwa ga ma’aikata maza waɗanda matansu suka haihu na tsawon kwanakin aiki 14.”
Sanarwar ta ƙara da cewa ba za a iya ɗaukar hutun fiye da sau ɗaya ba a cikin shekara biyu.
Haka nan za a iya ɗaukar hutun ne na haihuwa huɗu.