Home Labarai Gwamnatin Tarayya za ta dawo da shirin ciyar da dalibai a makarantu – Edun

Gwamnatin Tarayya za ta dawo da shirin ciyar da dalibai a makarantu – Edun

0
Gwamnatin Tarayya za ta dawo da shirin ciyar da dalibai a makarantu – Edun

Ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun ya ce gwamnatin tarayya na shirin dawo da tsarin ciyar da daliban makarantu da aka dakatar.

Edun, ya ce gwamnati za ta tabbatar akwai isassun kudade domin tallafawa da kuma dorewar shirin.

Ministan na bayanin hakan ne a yayin da kwamitin majalisar wakilai a fannin ilimi ya ziyarce shi a ranar Alhamis, acewar sanarwar da daraktan yada labarai na ma’aikatar kudi, Mohammed Manga ya fitar.

Sanarwar ta ce an gudanar da ganawar ne domin lalubo hanyoyin magance matsalar yaran da basa zuwa makaranta a Nijeriya.

Da yake jawabi a ganawar, Edun ya jaddada kokarin gwamnati na bunkasa fannin ilimi.

Ya ce ta hanyar tsare-tsare da ake samarwa kowanne yaro zai samu damar zuwa makaranta.

Ya ce, “Ciyar da yara a makarantu ba wai kawai yana bunkasa lafiyarsu bane, sai dai yana sawa su dinga zama a makaranta wanda hakan yake rage yaran da basa zuwa makaranta”.

A ranar 12 ga watan Janairu ne dai, shugaban kasa Tinubu ya dakatar da shirin na ciyar da dalibai a yayin da ake ci gaba da bincike a ma’aikatar jinkai da walwalar jama’a.

TheCable