Home Labarai Gwamnatin Tinubu za ta kammala aikin gas na AKK don bunƙasa tattatalin arziƙin Arewa

Gwamnatin Tinubu za ta kammala aikin gas na AKK don bunƙasa tattatalin arziƙin Arewa

0
Gwamnatin Tinubu za ta kammala aikin gas na AKK don bunƙasa tattatalin arziƙin Arewa

Gwamnatin Taraiya za ta ci gaba tare da gaggauta kammala aikin iskar gas na Ajaokuta zuwa Kaduna sannan ya dire a Kano, wanda aka yi wa laƙabi da AKK, inda aikin, in ji Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da kan Al’umma, Muhammad Idris, zai bunƙasa tattalin arzikin Arewacin Nijeriya.

Idris ya baiyana hakan ne a yayin wata ziyarar aiki da ya kai a cibiyar aikin ta Kaduna a jiya Juma’a tare da Ministan Kuɗi, Wale Edun da kuma Ƙaramin Ministan kula da Albarkatun Iskar Gas, Ekperikpe Ekpo da kuma shugaban kamfanin mai na ƙasa, NNPC, Mele Kyari.

A wata sanarwa da mataimakin Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da kan Al’umma, Rabiu Ibrahim ya fitar a jiya Juma’a, Ministan ya ce aikin gas din zai samar da hanyoyin bunƙasa tattalin arziki da dama a yankin Arewa.

A cewar Minista Idris, “AKK zai samar da wadatar da saukaka samun makamashi don amfani a gidaje, kamfanunuwa da masana’antu, sannan zai sauƙaƙa da kuma rage tsadar harkar sufuri.

“Ci gaba da kuma hanzarta kammala aikin gas na AKK, wanda shi ne mafi girma a tarihin Nijeriya da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta yi wata manuniya ce ga ƙoƙarin gwamnatin sa na ganin ta bunƙasa masana’antu da tattalin arzikin ko wanne yanki na ƙasar nan,” in ji shi.

Ya kuma yaba da aikin na AKK, inda ya ce wani ɓangare2ne mai matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa masana’antu da tattalin arziki wanda na ɗaya da ga cikin ƙudire-ƙudiren gwamnatin Tinubu.

Ministan ya kuma nuna cewa aikin zai samar da tsaro a yankin Arewa wanda rashin aikin yi ya ta’azzara, inda ya ce matasa za su samu haɓakar aikin yi da bunƙasar tattalin arziki.