Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha yayi kira ga ‘yan Najera da su goyi bayan sake tsayawa takarar Shugaba Buhari ta Shugaban kasa a 2019. Yace dukkan Gwamnonin Najeriya in banda guda biyu duk suna goyon bayan Shugaba Buhari ya sake yin takarar Shugaban kasa karo na biyu a zaben 2019.

Gwamna Okorocha yana fadin haka ne, lokacin da ya gabatar da wani jawabin gaban Shugabannin wata kungiyar matasa dake rajin ganin an sakezabar Shugaba Buhari a karo na biyu a 2019, wanda suka kai masa ziyara a gidan Gwamnatinjihar Imo dake birnin Owerri a ranar talatar da ta gabata.

“Shugaba Buhari shi yafi kowa dacewar tsayawa zaben Shugaban kasa a karo na biyu, babu wani dan takara da ya kai shi cancanta, don haka ba mu da wani zabi sama da shi”

“Ni na gamsu da Shugaba Buhari, dan haka ne ma tun shekaru da suka gabata nace, matukar Buhari zai yi takarar Shugaban kasa, to ba zan taba yin takara tare da shi ba”.

“Yanzu Allah ya bamu shi a matsayin shugaban Najeriya, dan haka, mu shaida ne na yadda buhari yake zaman daya tilo da zai iya magance matsalolin kasarnan, dan haka ne muke ganin, shi yafi dacewa a wannan lokacin”

Haka kuma, Mista Okorocha ya cigaba da cewa, ficewar Najeriya daga halin matsin tattalin arziki, na daya daga cikin dumbin dalilin da suka sanya muke goyon bayan Buhari ya sake tsayawa karo na biyu.

Ayayin da yake wannan kiran na sake goyon bayan Buhari ya yi shugabanci karo na biyu, ya kuma ce, Buhari ne kadai zai iya tabbatar da Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa mai bin tafarkin Demokaradiyya.

“Dan haka kada mutane su yi la’akari da zaben da aka gudanar a jihar Anambra, su sami sarewar guiwa kan goyon bayansu ga Buhari, domin wannan zaben ba shi da alaka da farin jinin Buhari”

“Su kansu Gwamnatin Ananbra da mutanan jihar Anambra suna goyon bayan Buhari, abin da ya faru na faduwar APC a jihar, wata ‘yar matsala ce tsakanin shugabannin APC a jihar, dan haka ba komai bace”

A yayin da yake mayar da jawabi, Shugaban kungiyar Kassim Kassim, yace, sun zo Owerri ne domin neman goyon bayan Okorocha kan takarar Shugaban kasar.

Sannan yace, Gwamna Okorocha shima ya cancanci ya yi takarar Shugaban kasa, dan haka idan Okorocha ya marawa Buhari baya dan kammala muhimman ayyukan da ya faro zai taimakawa al’ummar najeriya sosai.

“Bisa la’akari da irin ayyukan da ka yi a baya, kai yafi cancanta kayi takarar shugaban kasa a 2019, amma kash, mun riga mun ayyana goyon bayanmu ga Shugaba Buhari a 2019, dan haka ne ma, muke fatan kai ne zaka jagoranci wannan tafiya tamu”

“Dan haka ne, muke rokonka da ka jagoranci dukkan gwamnonin APC wajen mara baya ga takarar Shugaba Buhari a karo na biyu, duba da la’akari da irin dumbin ayyukan da yayiwa Najeriya, da kuma wadan da ake sa ran zai yi nan gaba”.

NAN