
Wani lauya kwararre kan kundin tsarin mulki, Kayode Ajulo, ya ce gwamnoni uku daga Arewa sun amince su goyi bayan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, LP, Peter Obi.
Ajulo ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa a Abuja a yau Juma’a, game da babban zaben 2023.
Sai dai ya lura da cewa Obi ba ya yi da jiki game da burinsa na takara saboda bai kai ga tuntuɓar masu ruwa da tsaki a fadin kasar nan ba.
“Har yanzu zan ce Peter Obi bai shirya zama shugaban kasa ba saboda bai shirya tsallakawa kogin Neja ba har ma da kogin Owena,” in ji Ajulo.
Ya ce gwamnoni uku sun ba da alamun cewa za su goyi bayan yunkurinsa na zama shugaban Najeriya a 2023.
Ajulo ya ce akwai bukatar a yi amfani da lokacin, inda kafin a fara yakin neman zabe na hakika ya isa yankin arewacin kasar.
“Ina sane da gwamnoni uku daga Arewa da suka ba da alamun goyon bayansa.”
Ya bukaci Obi da ya wuce kudancin Najeriya ya kai ga yankin arewa, domin “sayar da kansa ga mutanen arewa na iya canza labarin.”