
Wata Hajiya ƴar jihar Kaduna, mai suna Asma’u Ladan ta rasu a birnin Makkah a jiya Juma’a bayan gajeriyar rashin lafiya.
Yunusa Abdullahi, kakakin hukumar alhazai ta jihar Kaduna ne ya shaidawa kamfanin Dillancin labarai hakan a yau a sanar a filin Arfa.
Abdullahi ya ce tuni a aka shaida wa dangin marigayiyar, inda kuma mahukunta da ma’aikatan hukumar su ka taya su kaje da yi musu ta’aziyya.