Daga Yasir Ramadan Gwale

A dazu ne jirgi ya sauka da rukuni na karshe na alhazan jihar kaduna a filin sauka da tashin jiragen saman kasa da kasa dake Kaduna, da alhazan jihar daga kasa mai tsarki, abinda ya kawo adadi na karshe da suka dawo gida Nigeria daga mahajjatan jihar da suka sauke farali a bana.

Babban jami’in hulda da jama’a na hukumar kula da jin dadin alhazan jihar Kaduna Yunusa Muhammad Abdullahi ya bayyana hakan ga manema labarai. Inda yace da misalin karfe 7:05am na safiyar alhamis jirgi na karshe ya sauka da rukunin karshe na alhazan jihar Kaduna, wanda jirgin Med-view ya yi jigilar wasu daga cikinsu.

Jirgin na karshe dai ya sauka ne da manya manyan jami’an hukumar aikin hajji ta jihar Kaduna da sauran manyan mutane da suka hidimtawa alhazan a kasa mai tsarki ciki har da Imam Hussaini Sulaiman Tsoho Ikara da sauran wadan da gwamnati ta wakilta domin aikin alhazai.

Jirage guda biyu ne Max Air da kuma Med-View suka yi jigilar Alhazan jihar Kaduna, jirgin Max ya kwashi kimanin mutane 2,173, yayinda Med-View ya yi jigilar mutane 4,542.

Rahotanni sun bayyana cewar kimanin mutane 6,713 ne suka sauke farali a kasa mai tsarki daga jihar Kaduna.

Jagoran Alhazan na jihar Kaduna yabawa gwamnatin jihar Kaduna a bisa gudunmawa da kuma dukkan kulawa da ta baiwa Alhazan jihar a cewar Imam Sulaiman Tsoho Ikara, karkashim jagorancin Sakataren Gwamnatin jihar Kaduna Alhaji Balarabe Abbas Lawal da dukkan sauran wadan da suka taimaka wajen yiwa alhazai hidima a kasa mai tsarki, a yayin aikin hajjin bana.