
Allah Ya yi wa Barden Kano, Hakimin Bichi, Malam Idris Abdullahi Bayero rasuwa a yau Laraba a jihar Kano.
Daily Nigerian Hausa ta samo labarin cewa tuni Sarkin Kano Khalifa Dr. Muhammad Sanusi II, ya jagoranci Sallar Jana’izar marigayi Barden Kano a fadar sa.
An haifi Alhaji Idris Bayero a 1934, a cikin gidan Sarkin Kano. Bayan yayi karatun addini, ya yi karatun boko, ya kuma halarci kwasakwasai da dama a fannin mulki (administration) a wurare da dama a kasar nan, har ya zama sakataren a majalisar sarki, sannan kuma daga baya ya zama sakataren karamar hukuma.
An nada marigayi Alhaji Idris Bayero Hakimci a 1990, a matsayin Dandarman, Hakimin Rimingado, bayan rasuwar yayan sa, Danburam Bello Bayero, dake hakimci a garin. Shekara biyu bayan nada shi, a 1992 aka aka daga likkafar sa ya zama Danburam, aka bar shi a dai Rimingado. Sai a shekara4 1997 aka mayar da shi Bichi, inda daga baya aka kara masa mukami, aka nada shi a matsayin Barden Kano.
Rasuwar Barden Kano Idris ta kafa wani tarihi a Masarautar Kano, domin daga kan sa, babu sauran wani dan Sarkin Kano Bayero da ke rike da rawani. Daga Kano Chiroman Kano Sunusi (Sarkin Kano Sunusi I) zuwa yau, duk wanda aka taba nadawa rawani, sun kare. Ya zama shi ne na karshe a yayan Sarki Bayero da ke rike da hakimci, a yanzu sai jikoki da yayan jikoki.
A tuna cewa a 2019, Sarkin Bichi na wannan lokacin, Aminu Ado Bayero ya tsige shi daga hakimcin tare da sauran hakimai biyar.
Bayan dawowar Sarki Sanusi a karo na biyu, sai ya maida shi a matsayin Hakimin Bichi, amma saboda tsufa da kuma rashin lafiya, sai ɗan sa ne ya ke wakiltar shi a matsayin Hakimin na Bichi.