Shugaban kungiyar Boko Haram,Abubakar Shekau

Rundunar sojan sama ta Najeriya, ta bayar da sanarwar hallaka mai dakin shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau a jiya laraba. Runudnar tace matar ta halaka ne a yayin wani artabu da rundunar tayi da wasu ‘ya ‘yan kungiyar ta Boko Haram a kauyen Durwawa a wajen garin Konduga.

mai magana da yawun rundunar sojan sama ta kasa, Olatokunbo Adesanya, ya bayyana cewar jami’ansu sun hallaka Mallam Fatdasi, wadda ta wakilci mijinta Abubakar Shekau a yayin wannan gwabzawa da sojan saman suka yi da mayakan Boko Haram.

Ya kara da cewar, rundunar ta ci nasarar farwa mayakan kungiyar da dama, kuma an fatattake su daga kauyen Durwawa a yayin arangamar da ta yi sanadiyar mutuwar matar Abubakar Shekau.

Ya cigaba da cewar, wannan harin ya janyowa ‘yan kungiyar ta Boko Haram koma baya mai yawa, sabida irin muguwar illar da sojan suka yi musu. Sai dai har yanzu ana kokarin tabbatar da cewar, matar da aka kashe din ko ita ce sahihiyar mai dakin shugaban kungiyar Boko Haram din, Abubakar Shekau.