Categories
Raayi

Hanyoyin Magance Rikicin Siyasa A Jihar Kano

Jihar Kano ta sha fama da rikicin siyasa wanda ya ke faruwa kama daga zaɓen ƙananan hukumomi, zaɓen jiha ko ma na tarayya. A shekarun baya an yi  kashe- kashen manya ƴan siyasa, fyaɗe, kisan gilla, ƙone-ƙone da faɗan ƴan daba. Jihar ta fara samun kanta a tarzomar siyasa ne tun kafin karɓar ƴancin ƙasar nan. An sami rikici shekarar 1953 wanda ya biyo bayan cecekucen cewar yankin kudancin ƙasar nan suna son a baiwa Najeriya ƴanci a shekarar 1956, su kuma arewa basu shirya ba. Wannan ya harzuƙa matasa yin tarzoma suka afkawa inyamurai mazauna Kano inda aka sami asarar rayuka kusan 52 a lokacin.
A jamhuriyya ta biyu wajejen 1979-83 an yi faɗace-faɗacen ƴan bangar siyasa tsakanin mabiya Marigayi Mallam Aminu Kano, jagoran jam’iyyar PRP na ƙasa waɗanda ake yiwa laƙabi da ‘ƴan taɓo’ da kuma masu goyon bayan gwamnan Kano na wancan lokaci wato Marigayi Alh Muhammadu Abubakar Rimi, wato ‘ƴan santsi’. Shi ma an yi asarar dukiya da kuma rayuka da dama inda hatta wata tarzoma da ta faru a 1981 ta yi sanadiyyar rasuwar mai baiwa gwamna Rimi shawara a harkokin siyasa wato Dr. Bala Muhammed.
A Zaben 2011 an sami wata tarzomar siyasa bayan baiyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa musamman cikin Birnin kanon. Farko tarzomar ta faro ne da faɗa da jami’an zaɓe da kuma wasu manya ƴan jam’iyyar PDP da ma wasu ƴan jamiyyar ANPP.  misali an Ƙona gidan tsohon kakakin majalisar tarayya Alh Ghali Umar Na-Abba, an kai hari gidan Alh Bashir Tofa wanda shi kuma jigo ne a jam’iyyar ANPP da sauran wasu daidaikun mutane. A ƙarshe ma tarzomar ta koma ga duk wanda aka gani da abin hawa mai kyau bai tsira ba.
Ƴan siyasa suna ɗaukar ƴan banga a matsayin masu kare lafiyarsu, suna tsamo
su ne daga cikin ƴan daba, suna ba su makamai kama daga takobi, sanda,  gariyo da sauransu. Basu da tsarin albashi ko na alawus sai dai akan basu abin da ya samu, wani lokaci ma watsa musu kuɗin ake inda za su daka wawa kowa ya sami rabonsa, domin dai su sami kuɗin kashewa kama daga na abinci, zuwa ga sayen kayan maye wanda shi ne zai gusar musu da hankali domin aiwatar da duk wata aika-aika da kan biyo baya. Matasa ne marasa Sana’a, waɗanda ba su sami damar samun karatun addini ko na zamani ba. Matasa ne da ba su sami tarbiyyar iyaye ko ta al’ummar da suke rayuwa a cikinta ba.
 Hanyar mulkar jama’a ta hanyar daidaita al’amura kowa ya ji anayi da shi don a zauna lafiya shi ne siyasa. Amma ƴan siyasar ƙasar nan sun mayar da siyasa hanyar mulkar jama’a bisa son ran su domin biyan buƙatarsu. Basu damu da buƙatu da muradun jama’ar da suka zaɓe su ba. Sam zaman lafiyar talakan da ya zaɓe su baya gabansu ko kaɗan. Ƴan siyasa suna haba-haba da al’umma ne kawai idan an zo neman ƙuri’a. Ƴan siyasarmu ba sa yi mana adalci ko kaɗan, in dai akan mulkinsu ne ba su ƙi uban kowa ya mutu ba, amma sun ɓoye iyalansu a gida sun tura ƴaƴansu karatu ƙasar waje suna amfani da ƴaƴan talakawa suna kashe kawunansu.
Lallai akwai buƙatar a sake salon yaƙin neman zaɓe a jihar Kano da sauran jihohinmu na arewa duba da yadda ake salwantar da rayuka, asarar dukiya da firgici a tsakanin al’umma. Wajibi ne siyasar mu ta waye. Ya kamata mu kwaikwayo yadda ake gudanar da yaƙin neman zaɓe a zamanance cikin lumana da kwanciyar hankali, mutunta juna dama kishin ƙasa da addininmu.
Rikicin siyasa ya kasu kashi uku:
1. RIKICI KAFIN ZAƁE:
Wannan yana faruwa ne lokacin yaƙin neman zaɓe. Faɗa kan ɓarke tsakanin magoya bayan ɓangarorin jam’iyyu. Ko ƙone-ƙonen gidajen ƴan takara ko na magoya baya.
2. RIKICI LOKACIN ZAƁE:
Shi ne rikicin da kan ɓarke wajen jefa ƙuri’a inda akan sace akwatunan zaɓe, ko ƴan bangar siyasa su tarwatsa masu jefa ƙuri’a. Akan raunana mutane da jami’an zaɓe. Kayan aikin zaɓe kan salwanta a irin wannan tarzoma.
3. RIKICIN BAYAN ZAƁE:
Wannan rikicin ya fi mune kuma yana afkuwa ne bayan an bayyana sakamakon zaɓe. Ya kan rikiɗe ya zama babbar tarzoma inda ya ke zama barazana ga harkokin yau da kullum da tattalin arzikin al’umma.
Domin magance dukkanin irin waɗannan rkice-rikice, wajibin gwamnatoci ne samarwa da matasa ayyukan yi domin magance tsabagen talauci da ya yi katutu a tsakaninsu. Wasu matasan kuma suna buƙatar samar musu da yanayi mai kyau ne domin inganta sana’oinsu don dogaro da kai wanda zai rage zaman banza inda ƙarshe suke faɗawa ayyukan daba.
1. Akwai buƙatar sarakuna waɗanda su ne iyayen al’umma su tsawatar da dukkanin ɓangarorin ƴan siyasa akan buƙatar haramta shigo da ƴan banga /daba harkokin yaƙin neman zaɓe.
2. ‎Malaman addini nauyi ne akan su jan hankali da tunatarwa ga al’umma su guji shiga rigingimun siyasa.
3. Ƙungiyoyin masu kare haƙƙin ɗan adam da ƙungiyoyin matasa dole su shigo ciki domin wayar da kan al’umma akan hatsarin shiga fitintinun zaɓe ga matasa.
4. ‎Kafafen watsa labarai aikinsu ne su wayar da kan al’umna akan illar dake tare da rikicin zaɓe.
5. ‎Hukumar ƴan sanda wajibi su yi aikin da aka ɗauke su akai wanda shi ne: Kare dukiya da rayukan al’umma a kowane lokaci ba tare da goyon bayan wani ɓangare ko jam’iyya ba.
6. ‎Hukumar zaɓe ta jiha wato  KANIEC da kuma ta ƙasa wato INEC dole su tsaya akan gaskiya da adalci, wajen gudanar da zaɓe da wajen bayyana sakamakon don gudun rikici.
7. ‎Dole ƴan siyasa su tsawatar da magoya bayansu cewar harkar siyasa ba ta a ‘mutu ko a yi rai’ ba ce. Kuma su guji yin amfani da matasa, ƴaƴan talakawa wajen aikin bangar siyasa.
8. ‎Hana bayyana sakamakon zaɓe a kafafen sadarwa na zamani, misali fesbuk da tiwita, domin yana kawo ruɗani da kawo sakamkon ƙarya.
A ƙarshe muna fatan za a gudanar da dukkannin zaɓuɓɓuka masu zuwa cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *