Tsohon wakili a cikin kwamitin amintattun jam’iyyar APC, Sanata Francis Okpozo, na daya daga cikin jerin sunayan mutanan da Shugaba Buhari ya baiwa mukamai na shugabannin ma’aikatun Gwamnati a ranar juma’ar da ta gabata.

Mista Okpozo, tsohon Sanata, wanda ya mutu a ranar 26 ga watan Disambar 2016, abin mamaki, yana daya daga cikin mutanan da aka baiwa mukamin Shugaban Nigerian Press Council.

Sakataren Gwamnatin tarayya  Boss Gida Mustapha ne dai ya bayyana sunayan mutanan da aka baiwa sabbin mukaman, kuma shi ne ya sanar da sunan Okpozo a matsayin daya daga cikin sabbin shugabannin, shekara daya bayan mutuwarsa.

Haka kuma, tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin rusasshuyar jihar Bendel wanda ya mutu a jihar Edo bayan yasha fama da jinya, an kuma zabe shi a matsayin sanata a jam’iyyar SDP.

Mista Okpozo, shi ne tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Bendel a karkashin rusasshiyar jam’iyyar UPN.

Ya mutu yana da shekaru 81 a wani asibiti mai zaman kansa a birnin Benin na jihar Edo, yayin daga bisani aka kaishi asibitin koyarwa na jami’ar Benin.

Bayan haka kuma, wata kafar sadarwa ta yanar gizo ta jiyo mai Magana da yawun Shugaban kasa, Femi Adeshina yana nuna juyayi da alhinin mutuwar Okpozo a madadin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda yake cewa “Iyalai da ‘yan uwan marigayi Sanata Okpozo, wanda ya karar da rayuwarsu wajen yin kira ga adalci da daidaito musamman a yankin Neja Delta, a iyaka tsawon rayuwarsa ta hidima day a yiwa al’ummar yankinsa”

Bayanin ya cigaba da cewar, “Yana daya daga cikin jiga jigan jam’iyyar APC a yankin kudu maso kudu, Shugaba Buhari da kansa yace, Jam’iyyar APC ta amfana matuka daga cikin baiwar Okpozo”