Home Labarai Har yanzu ana ci gaba da karɓar takardun Naira, inji CBN

Har yanzu ana ci gaba da karɓar takardun Naira, inji CBN

0
Har yanzu ana ci gaba da karɓar takardun Naira, inji CBN

Babban bankin Najeriya, CBN, ya ce har yanzu takardun kudi na Naira, tsoffi da sababbi halastattu ne kuma ana ci gaba da karɓar su.

Babban bankin ya yi wannan bayani ne kan labarin rashin isassun kudade, da kin karɓar tsofaffin takardun kudi a wasu sassan kasar.

Bankin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bankin, Isa AbdulMumin ya fitar, kuma ya wallafa a shafinsa na X a jiya Laraba.

Sanarwar ta ce: “Don kauce wa shakku, yayin da muke nanata cewa akwai isassun takardun naira a fadin kasar nan don gudanar da duk harkokin tattalin arziki na yau da kullum, muna so mu bayyana babu shakka cewa duk wata takardar kudi da babban bankin Najeriya ya fitar ta kasance halastacciya kuma ba a dena karba ba, kamar yadda sashe na 20 (5) na dokar CBN, 2007 ya bayyana.

“Saboda haka, an umurci rassan bankin na CBN a fadin kasar nan da su ci gaba da fitar da takardun kudi daban-daban na tsofaffi da wadanda aka canza musu fasali a cikin adadi mai yawa zuwa Bankuna don ci gaba da rarrabawa ga abokan huldar bankuna.

“Muna so mu sake bayyana cewa duk takardun kudi na banki da CBN ke bayarwa suna nan a kan doka. Kamar yadda sashe na 20 (5) na dokar CBN ta shekarar 2007, babu wanda ya isa ya ki karbar Naira a matsayin hanyar biyan kudi.”