Home Labarai Har yanzu ban saki sana’ar ɗinki ba, in ji ƴar majalisar wakilai a Kwara

Har yanzu ban saki sana’ar ɗinki ba, in ji ƴar majalisar wakilai a Kwara

0
Har yanzu ban saki sana’ar ɗinki ba, in ji ƴar majalisar wakilai a Kwara

Ƴar majalisar dokokin jihar Kwara, mai wakiltar mazabar Owode/Onirin daga karamar hukumar Asa Ruqayat Shittu, ta ce har yanzu ta na zuwa shagonta na ɗinki bayan ta tashi daga ofishin ta.

‘Yar majalisar mai shekaru 26, da ake kyautata zaton ita ce ƴar majalisa mafi karancin shekaru a Najeriya, a wani sakon da wakilin Daily Trust ya gani a shafinta na Facebook a jiya Talata, an ganta a wani faifan bidiyo ta na aiki a kan kenan ɗinki a shagonta.

Ta ce, “Duk da kasancewa ta jami’ar gwamnati, har yanzu ina aiki na na ɗinki. Kamar yadda duk kuka sani, ni ƙwararriyar tela ce kuma har yanzu ina yinwa kwastomomi na dinkuna iri-iri. ”

Ta wallafa da yaren yarabanci: Ise ni ogun ise, Ise ni fin di eni gi ga (kasancewa mai hankali da mai da hankali yana kai ka ga kololuwar nasarar sana’arka). Yi aiki, don Allah a yi aiki.”

Ruqayat wacce ta kammala karatun digiri na biyu a fannin sadarwa na zamani a shekarar 2022 daga Jami’ar karatu daga nesa, NOUN, Ruqayat ita ce Shugabar Kwamitin Majalisar Matasa, Wasanni, Watsa Labarai da Yawon shakatawa a Majalisar Kwara ta 10.