Home Ƙasashen waje Harbin da a ka yi a makarantar Texas ya bani takaici matuƙa — Fafaroma

Harbin da a ka yi a makarantar Texas ya bani takaici matuƙa — Fafaroma

0
Harbin da a ka yi a makarantar Texas ya bani takaici matuƙa — Fafaroma

 

Fafaroma Francis ya bayyana cewa ransa ya matuƙar ɓaci da harbin da aka yi a wata makaranta a Texas, wanda ya yi sanadiyar kisan akalla yara 19 da malamai biyu, inda ya yi kira da a kara tsaurara matakan kan kula da makamai.

Fafaroma ya magantu ne game da harbin da aka yi a Uvalde, Texas, “Na ji takaici da kisan kiyashin da aka yi a makarantar firamare a Texas. Ina yi wa yara da manyan da aka kashe da kuma iyalansu addu’a.

“Lokaci ya yi da ya kamata a tsayar da fataucin makamai. Mu dage mu dage domin kada irin wannan musiba ta sake faruwa.’’

Da yake magana daga Fadar shugabancin kasar Amurka sa’o’i bayan harbe-harben, shugaban da a fili ya girgiza, Joe Biden ya bukaci Amurkawa da su tashi tsaye wajen nuna goyon baya wajen gyara dokar riƙe makami a maida ita mai tsauri.

Francis ya sha sukar masana’antun makamai.

Ko a shekarar 2015 ya ce mutanen da ke kera makamai ko saka hannun jari a masana’antar makamai munafukai ne idan har su ka kira kansu Kirista.