Shugaban kungiyar Boko Haram,Abubakar Shekau

Jami’an ‘yan sanda a jihar Adamawa, sun ce adadin mutanen da suka rasu a sakamakon mummunan harin kunar bakin wake a wani Masallacin ‘yan Shuwa a karamar hukumar Mubi ta Arewa ya kai mutum 50.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda jihar Adamawa,  Othman Abubakar, ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN wannan al’amari a harin ranar talatar nan.

Othman Abubakar yace, wani karamin yaro ne ya tayar da Bom din a masallaci yayin da ake gudanar da Sallar Asubahi.

“Muna da gawarwakin mutum 50 a hannunmu yanzu haka, muna fatan samun adadin mutanan da suka samu raunuka a wannan hari” Inji jami’in hulda da jama’ah na rundunar ‘yan sandan jihar ta Adamawa Othman Abubakar

Da sanyin safiyar talatar nan, Shugaban karamar hukumar Mubi ta Arewa Musa Bello yace, jami’an asibitin sun shaida masa rasuwar mutum 22 a yayin wannan hari.

Kamfanin dillancin labarai na najeriya, ya ruwaito cewar wannan hari ya auku ne a yankin Dazala na karamar hukumar Mubi ta Arewa a ranar talatar nan da misalin karfe 5 na asubahi, yayin da ake Sallar Asubah.

Wannan hari dai shi ne irinsa karo na uku a yankin karamar hukumar Mubi ta Arewa tun bayan da rundunar sojin Najeriya ta kwato garin na Mubi daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram.

NAN