Home Ƙasashen waje Hausawan Sudan na zanga-zanga kan kisan ƴan uwansu

Hausawan Sudan na zanga-zanga kan kisan ƴan uwansu

0
Hausawan Sudan na zanga-zanga kan kisan ƴan uwansu

 

Al’umar Hausawa mazauna Sudan sun gudanar da zanga-zanga a biranen kasar da dama, domin nuna bacin ransu, game da kisan da aka yi wa ‘yan uwansu a rikicin kabilancin da ya barke ‘yan kwanakin nan a kasar.

BBC Hausa ta rawaito ta bakin Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa hukumomi sun ce mutum 79 ne aka kashe sakamakon rikicin na kabilanci tsakanin Hausawa da ‘yan kabilar Berti a jihar Blue Nile.

AFP ya ruwaito cewa daruruwan Hausawa ne suka fito zanga-zangar a Khartum birnin kasar rike da kwalayen da ke dauke da rutubun neman adalci ga ‘yan uwansu da aka kashe.