26.8 C
Abuja
Friday, July 1, 2022

Hisbah za ta ɗauki sabbin ma’aikata 3,500

Must read

 

 

 

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce zata dauki sabbin ma’aikata 3500 a fadin jihar.

Babban Kwamandan hukumar, Sheikh Muhammad Sani Ibn Sina ne ya bayyana wa manema labarai a Kano a jiya Talata.

Ibn Sina yace wannan na zuwa ne bayan sahalewar da hukumar ta samu daga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, a wani mataki na kara inganta ayyukan hukumar ta Hisbah.

Babban kwamandan yace tsarin daukar sabbin ma’aikatan zai baiwa ‘yan Hisbah na sa kai da ake kira ‘Hisbah Marshal’ fifiko, kana daga bi sani sauran mutane su shigo ciki.

“Kaso saba’in cikin dari za su kasance cikin Hisbah Marshal wanda shakka babu mun gamsu da irin kokari da gudunmawa da suke baiwa hukumar Hisbah daga daukar su zuwa yanzu.

“Sai kuma shalkwatar hukumar ta Hisbah cikin tsarin jadawalin za ta dauki mutane dari biyar, sai kananan hukumomi na kwaryar birnin Kano guda takwas za su dauki dari-dari, sai kuma sauran kananan hukumomi da za su dauki hamsin-hamsin kowannen su.

Babban kwamandan hukumar ya kuma ja hankalin al’umma da su kaucewa fadawa komar bata gari wajen karbar kudin sun don sa su cikin tsarin ma’aikatan da hukumar za ta dauka nan ba da dadewa.

“Duk mai son samun wannan dama to ya garzaya karamar hukumar sa, daga nan ne za’a dauka don turo mana sunayen mutane mu tantance”, Harun Muhammad Sani Ibn Sina.

 

latest news in nigeria today 2022 punch

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article