
Rundunar Hisbah ta jihar Yobe ta kama wasu mutane 14 da ake zargi da laifin karuwanci da safarar miyagun kwayoyi.
Yusuf Yusuf, babban sakataren ma’aikatar harkokin addini ta jihar ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai a yau Talata a Damaturu.
Yusuf ya ce wadanda ake zargin sun hada da mata tara da maza biyar, ya kara da cewa an kama su ne bayan wani samame da aka kai a Damaturu da suka hada da Gidan Ajayi, Zango, Bus Stop, da sauransu.
Ya kara da cewa wasu daga cikin wadanda ake zargin za a mika su ga jami’an tsaro domin gurfanar da su gaban kuliya, yayin da sauran kuma za a yi musu nasiha kan gyaran halaye.
“Wasu kuma za a yi musu nasiha daga malaman addinin Musulunci, da fatan gyarawa,” inji shi.