Hukumar Hisbah ta jihar Sakkwato, ta nuna damuwarta akan sakacin iyaye wajen yawaitar fyaden kananan yara a jihar. A ranar Alhamis, hukumar ta bayyana cewar, ta samu rahotanni 59 na yaran da aka yiwa fyade a shekarar 2017, tace kuma a mafiya yawan lokuta akwai sakacin iyaye wajen yiwa yaran nasu fyade.

Shugaban hukumar, Adamu Kasarwa, shi ne ya bayyanawa kamfanin dillancinlabarai na Najeriya NAN, cewar a jihar Sakkwato, wasu iyayan da dama basu cika damuwa kan inda yaransu suke zuwa ba, ko kuma das u waye suke mu’amala, dan haka ake yawan samun laifin fyade ga kananan yara sabida sakacin iyayansu.

Ya kara da cewar, “Sabida sakaci, wasu iyayan suna barin yaransu mata kankana,suna mu’amala da samari masu yi musu hidima a gida, har abin ya wuce lissafi, ta yadda a karshe irin wadannan masu yin aikatau kan kare da yiwa yaran fyade”.

Malam Adamu ya kara da cewar, Duk da cewar yara 59 aka samu rahotannin yi musu fyade a wannan shekarar ta 2017, amma hakan ya nuna raguwar ayyukan fyade a wannan shekarar, domin a shekarar bara ta 2016, an samu rahotonannin fuade guda 159, abinda yake nuna an samu raguwa sosai.

Sannan kuma, ya zargi masu unguwanni da dagatai, da karbar toshiyar baki, domin danne maganar gyade da ake kawowa gabansu a kauyukansu.

Y ace “A wasu kauyukan, su masu unguwanni ko dagatai da kansu, suke neman a basu dan na goro domin su danne maganar, sannan sukan yiwa iyayan da aka yiwa ‘yarsu fyade barazana da kada su kuskura su sanar da jami’an tsaro idan an yiwa ‘yarsu fyade”

Shugaban hukumar ya cigaba da cewar, rahotannin fyade da aka samu a wannan shekarar an mika su zuwa ga hukumar kula da hakkin kananan yara ta kasa NAPTIP da hukumar ‘yan sanda domin duba yuwuwar abinda ya dace.