
Hukumar kula da shige da fice ta ƙasa, NIS, ta dakatar da wani jami’inta mai mukamin ASI 2, Okpravero C. Ufuoma dake aiki a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas.
An kama jami’in ne a wani bidiyo da aka hango shi ya na rokon kuɗi a wurin matafiya.
A sanarwar da Kwanturola Janar ta hukumar, Kemi Nandap ta fitar, ta ce abinda jami’in ya yi ya saɓa dokar aiki ta hukumar ta NIS.
Sanarwar ta ƙara da cewa an samar da na’ura a dukkan filayen jirgin sama domin lura da irin ayyukan jami’an hukumar.
A don haka hukumar ta sanar da dakatar da shi har zuwa lokacin da za a kammala bincike.
Hukumar ta ce ta himmatu wajen kawar da masu cin hanci da rashawa a ma’aikatan ta.
NTA