Home Labarai Hukumar Kwastam ta gargadi yan Nijeriya kan daskararrun kaji da aka shigo da su daga Kwatano

Hukumar Kwastam ta gargadi yan Nijeriya kan daskararrun kaji da aka shigo da su daga Kwatano

0
Hukumar Kwastam ta gargadi yan Nijeriya kan daskararrun kaji da aka shigo da su daga Kwatano

Hukumar Kwastam ta Kasa, reshen Jihar Ogun ta gargadi yan kasa akan cin wasu daskararrun kaji da talo-talo da aka yi fasa-kaurinsu uwa cikin kasar.

Kwantarola na jihar, James Ojo, wanda yayi gargadin ga manema labarai a yau Litinin ya kuma ce daskararrun tsintsayen na da illa ga lafiyar jiki.

ya ce tsuntsayen da aka shigo da su daga Jamhuriyyar Benin, an daskarar da su ne da wasu sunadaran magunguna kuma basu da cikakkun lasisi.

ya ce hakan ka iya kara hadarin kamuwa da cututtuka ga jikin yan Nijeriya.

ya yi bayanin cewa sashen abinci da noma na majalisar dinkin duniya ma ya yi gargadi kan cin daskararrun tsuntsaye da ake shigowada su daga kasashen waje.