Categories
Labarai

Hukumar NDLEA ta gano tabar wiwi ta miliyan 20 da aka noma ta a Najeriya

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta gano wata makekiyar gona da aka noma tabar wiwi a dajin Ugbubezi dake yankin karamar hukumar Owan ta yamma a jihar Edo.

Babban kwamandan hukumar NDLEA reshen jihar ta Edo, Buba Wakawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Benin a ranar Laraba.

Mista Wakawa yace, Jami’an hukumar tasu ne, suka gano wata ma’ajiya da aka tare jibgin tabar wiwi din da aka noma a wajen a dajin Ugbubezi.

Yace, wannan wiwin da aka kama darajarta ta kai kimanin naira miliyan 20, hukumar taci nasarar kwashe ta gaba daya daga inda aka ajiyeta ta hanyar yin amfani da jami’anta su 70.

Mista Wakawa ya cigaba da cewa, Sun ga manyan buhunhuna da aka dura tabar a ciki wanda nauyinsu yakai kilogiram 680 a cikin buhunhuna 94, wanda gaba daya nauyinsu yakai kilo 1,316.

Sai dai kuma, hukumar taci nasarar kame wasu mutum biyu da aka samu suna aiki a inda ake ajiye da tabar wiwi din.

Kwamandan hukumar NDLEA ya bayyana cewar, katafaren dakin da aka ajiye wannan tabar wiwi din, an gano shine sakamakon wani rahoton asiri da hukumar ta samu.

“Munyi aiki da bayanan sirrin da muka samu, kuma muka ci nasarar gano wajen wanda yake a karamar hukumar Owan ta yamma” A cewar Wakawa.

Mista Wakawa ya cigaba da cewar, dukkan mutanen biyu da aka kamaa, nan ba da jimawa ba za’a gabatar da su gaban kuliya.

Yace a bisa tanade tanaden dokokin hukumar NDLEA, duk wanda akakama da irin wannan laifi zai iya shafe akalla shekaru 15 a gidan kaso, sabida mallakar tabar wiwi.

 

NAN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *