
Hukumar tattara kuɗaɗen-shiga ta jihar Nasarawa, NSIRS, ta ce ta tara Naira biliyan 7.4 a matsayin kudaden shiga tsakanin watan Janairu zuwa Yuni na wannan shekara.
Shugaban hukumar, Ahmed Yakubu ne ya bayyana hakan a jiya Talata a garin Lafiya, lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin kuɗi da kasafi na majalisar dokokin jihar.
Ya shaida wa kwamitin cewa hukumar ta yi amfani da dabarun tattara kudaden shiga ta na’ura mai kwakwalwa, ta yadda za a toshe hanyoyin zurarewar kuɗi.
“Ina so in yaba wa kwamitin don tallafawa ayyukanmu don samun nasara.
“Mun taka rawar gani wajen samar da kudaden shiga domin mun samu sama da Naira biliyan 7.4 cikin watanni shida.
“Ina so in tabbatar muku da cewa za mu kara yin aiki don ɗorawa a kan haka da yardar Ubangiji,” in ji Mista Yakubu.