Categories
Labarai

Hukumar tsaro ta NSCDC a tura jami’an ta 3500 domin zaben kananan hukumomi a Kano gobe

Hukumar tsaro ta NSCDC reshen jihar Kano ta ware jami’anta kimanin 3500 domin sanya idanu a zaben kananan hukumomin da za a  yi a gobe Asabar.

Wannan na cikin sanarwar da hukumar ta bayar ta hannun kakakin hukumar, Ibrahim Idris wanda ya sanar  da hakan ga manema labarai.

“A kalla mutane 3500 ne hukumar tsaro ta NSCDC ta tura domin sanya idanu a zaben kananan hukumomin a jihar Kano” A cewar Mista Idris.

Yace jami’an zasu yi aiki da sauran jami’an tsaro domin zaben na kananan hukumomin jjihar kano, domin yin zabe cikin kwanciyar hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *