
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kaanta INEC ta yiwa sabbin jam’iyyu guda ashirin da uku rajista, abinda ya kawo adadin jam’iyyun siyasar Najeriya zuwa guda 91.
A cewar majiyar gidan talabijin na Chennels, sun ruwaito cewar hukumar ta kara makwanni biyu domin cigaba da yin rejistarkatin zabe a duk fadin Najeriya.
A baya dai hukumar ta bayyana cewar zata rufe rajistar yin sabon katin zabe ne a ranar 17 ga watan Agustan nan, sai bayan zaben shekarar 2019.