Home Labarai Hukuncin Kotun Daukaka Ƙara tabbatar da nasarar Abba Gida-gida ya yi ba korar sa ba — Gwamnatin Kano

Hukuncin Kotun Daukaka Ƙara tabbatar da nasarar Abba Gida-gida ya yi ba korar sa ba — Gwamnatin Kano

0
Hukuncin Kotun Daukaka Ƙara tabbatar da nasarar Abba Gida-gida ya yi ba korar sa ba — Gwamnatin Kano

Kwamishinan Shari’a kuma Antoni Janar na jihar Kano, Barista Haruna Dederi ya ce sun gano cewa ashe hukuncin Kotun Daukaka Ƙara tabbatar da nasarar zaɓen Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi ba korar sa ba.

A wani taron manema labarai a jiya Talata, Dederi ya ce hukuncin, gwamna Abba ya ce a baiwa Naira miliyan daya kuɗin tara ba wai shi ya bayar ba

Ya ce gwamnatin Kano ta gano cewa bayanin da su ke cikin kundin hukuncin ya saba da sanarwar da alkalami kotun daukaka kara suka yi a ranar Juma’a da ke tabbatar da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ta yanke.

Sai dai kuma Dederi ya ce sahihin kwafin na hukuncin kotun daukaka kara ya nuna cewa kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da kotun ta ƙasa ta yanke.

Dederi, wanda ya nuna mamaki da takaici a kan lamarin, ya ce za su rike wannan a matsayin shaida da za su kai korafinsu zuwa kotun koli.