
Kwamishinan Ilimi mai Zurfi na Jihar Kano, Dakta Yusuf Ibrahim Kofarmata ya baiyana cewa Allah ne Ya kwato wa Kanawa hakkinsu sakamakon nasar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu a Kotun Ƙoli.
A wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kan sa a yau Asabar a Abuja, Dakta Kofarmata ya taya Gwamna Yusuf murna, inda ya kara da cewa ƴar manuniya ta nuna cewa dama al’ummar Kano Abba Gida-gida su ka zaɓa.
A cewar Kwamishinan, Gwamna Yusuf zai yi iya ƙoƙarin sa ya saka wa Kanawa goyon bayan da su ke masa ta hanyar damar da aiyukan more rayuwa.
Ya kara da cewa tun a farkon mulkinsa, Gwamna Yusuf ya taka rawar gani, inda ya kasance daya daga cikin gwamnonin da su ka yi fice a Nijeriya wajen yi wa al’ummar su aiyukan ci gaba.
“Za mu dora daga inda muka tsaya. Gwamna Abba mai son al’ummar Kano ne kuma zai fitar da mu kunya,”
Ya ce Gwamna Abba na kawo aiyukan ci gaba ne domin shi mabiyin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, shugaban darikar Kwankwasiyya na ƙasa ne.
Ya yaba wa Madugun na Kwankwasiyya bisa yadda ya ke kaunar talakawa kuma ya ke ɗora mabiyansa a kan wannan turba.
Kwamishinan ya kuma tabbatar da cewa shi ma a ma’aikatar sa, zai iya yinsa wajen ciyar da makarantun gaba da sakandare gaba har su zamto sun yi kan-kan-kan da na sauran ƙasashe.